Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali

Tambayoyi da amsarsu tare da Mallam Ibrahim Zakzaky na takwas

Sayyed Zakzaky2

Ko ya halatta mutum ya yi addu'a don wani mukami?
TAMBAYA: Ko ya halatta mutum ya yi addu'a don neman mukami, kamar kansila ko waninsa?

Daga Usman Tumu Jihar Gombe

SHAIKH ZAKZAKY: To ita dai addu'a ibada ce, kuma duk abin da mutum ya roka wajen Allah, sawa'un na duniya ne ko na lahira, ya nuna ya san Allah ne Mai bayarwa don haka ya nema a wurinsa. Sai dai abin da ya fi alheri, shi ne mutum in yana neman abu, ya ce "Ya Ubangiji in ka san wannan shi ne mafi alheri gare ni a duniyata da lahirata da magaggabcin al'amarina da majirkincinsa, kuma shi ne a gare mu gyara kuma gare ka akwai yarda, to ka biya mana." Ya kamata ya sa sigar wannan. Saboda haka duk addu'ar da mutum zai yi, in dai ya roki Allah, ya ce, Allah in dai wannan al'amari akwai gyara, maslaha ne gare ni, kai kuma akwai yarda gare ka ka biya mani," to insha Allah zai ga biyan bukata kamar yadda Allah yake so.


TAMBAYA: Ana cewa duk wanda ya kashe wani kisan ganganci, to dukkan laifukan wancan suna kansa. Shin haka ne?

Daga Yakub Almafary

SHAIKH ZAKZAKY: A'a, ba haka bane, shi dai ya yi laifin kisan ganganci. Saboda haka laifin kisan gangancin ne ke kansa. Amma shi wancan wanda aka kashe, kyawawan ayyukansa nasa, munanan ayyukansa nasa.

TAMBAYA: Ko ya halatta mutum ya yi layya da dabbar da aka dandake?

Daga Shehu Garba Gidan Magajin Garin Kauran Namoda, Jihar Zamfara.

SHAIKH ZAKZAKY: Eh, za a iya yi, saboda dandaka ba tawaya ne ba. Abin da aka hana layya da shi, shi ne abin da ya sami tawaya wanda za a ce masa tawaya, wato bai kammala ba. Kamar a ce misali mai karyayyen kaho ko yankakken kunni ko gutsirarriyar kafa ko tamikakken dabba ko mara kitse, ko abin da ya yi kama da haka nan wanda shi wannan tawaya ne. Amma dandaka shi wannan kamar ma gyara nama ne da cikar dabba. Saboda haka bai maishe shi aibi ba. Wato a takaice dabbar da aka hana a yi layya da ita ita ce wadda take da aibi, shi kuwa dandaka ba aibi bane, gyara ne ma.

TAMBAYA: Menene hukuncin wanda ya yi sata yana yaro karami bai balaga ba? Shin laifin na kan iyayensa ne ko kuwa?

Daga Shehu Garba Gidan Magajin Garin Kauran Namoda Jihar Zamfara.

SHAIKH ZAKZAKY: Laifi ba zai iya hawa kan iyayensa ba sai idan iyayensu suka taimaka a kan yin laifin. In ba haka ba, shi yaro kafin ya balaga ba a rubuta masa laifi. Kamar yadda ya zo a hadisi cewa, an dage alkalami daga mutum uku, yaro har sai ya balaga, mai barci har sai ya farka, mara hankali har sai ya sami hankali. Saboda haka shi lallai laifi bai hau kansa ba, bai hau kuma kan iyayensa ba, sai dai idan su ne suka sa shi.

TAMBAYA: Ko ya halatta Malamin makarantar allo ya sa almajiransa noma idan suna zaune a karkara ne, in kuma a birane ne su ke karbar wani abu daga hannun yaran, musamman da yake ba biyan sa ake ba?

Daga Abubakar Sa'ad Barbaji Gidan Liman jihar Kano

SHAIKH ZAKZAY: To shi dai wajen koyar da yaro, an yarda a karbi lada wajen koyar da yaro karatun Alkur'ani. Saboda haka duk yadda ya zama yarjejeniya tsakanin Malami da uban yaro. Idan bangaren yarjejeniyar shi ne yaron zai yi aiki a gona, daidai gwargwadon aikin da ba zai hana shi karatu ba, ya zama bangaren ladan karantar da shi; in dai sun yi yarjejeniyar, babu laifi. Amma abin da aka sani dai shi ne, ana iya karbar lada. Amma dai ba a kayyade bayar da yanayin ladan ba.

TAMBAYA: Menene adalci ga wanda yake da mata biyu ko fiye da haka wajen daidata tsakaninsu, shin zai iya yi a kan abin da yake wajibinsa ko har ma da abin yake kyautatawa ne a gare su?

Daga Abubakar Sa'ad Barbaji Gidan Liman jihar Kano

SHAIKH ZAKZAKY: To har da na kyautatawan, domin kuwa idan ya biya wajibi sannan sai a nafila sai ya fifita wata, ya yi rashin adalci. Alal misali kamar a ce bayan ya yi suturar dole sai kuma ya yi kayan ado ya kebance wata da shi hususan, to ka ga rashin adalci ne wannan saboda in zamansu tare ne, zai zamo wata rana da labarin ya yi wa wancan kaza (ya je gare ta), kuma za ta ga ita ina nata? Saboda haka lallai daidai gwargwado duk abin da yake rabawa, sawa'un na dole ne ko na ihsani ne, duk dai ana son ya yi adalci.

TAMBAYA: Ko ya halatta ga mai mata biyu ko fiye ya fi kyautata wa daya saboda ta fi yi masa biyayya ko kuma saboda ita ya auro ta daga gidan masu wadata, saboda wasu na cewa wai kowace mace ana ba ta abinci gwargwadon yadda take samu a gidan su?

Daga Abubakar Sa'ad Barbaji Gidan Liman jihar Kano.

SHAIKH ZAKZAKY: Ba a ce wani abu mai kama da haka nan ba. Abin da aka ce dai kawai akwai abin da ake ce ma 'kafa'a'. Abin da ake ce ma 'kafa'a' shi ne daidai matsayi da ma al'ada. Alal misali kamar idan wasu abincinsu burabusko, wasu tuwo, to ka ga kowacce ita irin abin da ta saba ci ne za ta yi. Wannan ba yana nufin ana fifita wata ne ba. Saboda ita mai cin wancan, idan aka ba ta wannan za ta ga ba ta da bukata ne. Shi wannan ne kawai aka ce, amma ba ana nufin cewa, yanzu idan misali, sai in abinci mai dadi ne sai ya ce ai 'yar gidan masu wadata ne sai a ba ta abinci mai dadi. An ce maka in mutum ba shi da wadata ba ya cin abinci mai dadi ne? Saboda haka lallai ba nan ne kafa'a take ba. Kafa'a shi ne a al'adar mutum shi in ana masa wannan, ba ya ganin ma an kyautata masa ne, sai a yi masa abin da shi a wurinsa shi ne kyautatawa. Amma ka san 'yar talakawa ba za ta ce idan an ba ta abinci mai dadi ba a kyautata mata ba, a ba ta mara dadi. Saboda haka ya kamata a gane ma'anar kafa'a a sa ta a muhallinta.

TAMBAYA: Wasu na cewa Imamai Ma'asumai (AS) ba su zama ma'asumai ba sai ta hanyar aikin da suke yi. Shin wannan aikin da ya kai su ga samun wannan daraja, a nan duniya ne suka yi shi ko kuwa a ina ne?

Daga Ahmad Mando, Kaduna.

SHAIKH ZAKZAK: Su da ma can zababbun Allah ne wanda Allah (T) ya kyautata tarbiyyarsu, ya kuma yi su yadda ya dace da sakon da ya dora masu. Na'am su ma mutane ne. Saboda haka suna da wadansu abubuwa da suke bijiro masu irin na sauran mutane, amma su sun fi karfin su aikata laifuffuka. Saboda su a matsayinsu, ba zai yiwu ma su aikata laifin bane, saboda zuciyarsu ba irin na wanda za su so su yi laifin bane. Saboda haka ka ga in haka nan ne, sun kai mustawa ne da in suka yi abin kirki, ya zama abin yabo gare su. Wato ba wai an yi su ne kamar inji, wanda yake yana aikin kawai ba tare da ya san abin da yake yi ba. Suna da 'yancin zabi amma abu mai kyau suke zaba, ba su mummuna. Shi ya sa ka ga Allah (T) yana yabon bayinsa Annabawa a cikin Alkur'ani, kamar yadda yake yabon Ayyub, yake cewa "Inna wajadnahu sabiran ni'imal abd innahu awwab." Mun same shi mai hakuri da dauriya, madalla da bawa mai yawan komawa da al'amarinsa zuwa ga Allah. Da sauran yabo wanda aka yi wanda aka yi wa Annabawa, kamar Ibrahim da Isma'il da cewa shi mai cika alkawari ne, da ire-iren wadannan. Ka ga wato ayyuka kenan. Abin da nake fata shi mai tambayar ya fahimta shi ne, matsayin isma ba matsayi ne da kake tsuwurwurta da aikinka ba, wanda yake wanda wani wanda yake in ya so sai ya yi ta yin aikin kirki sai ya koma ya zama irin shi ba. Wato kamar annabci, ba ana yin aiki ne mai kyau sai a zama Annabi ba. Da ma su Annabawa zababbu ne tun asali. Haka ma matsayin Imamai, shi ma ba wani aiki ne mutum yakan yi in ya kai wani mustawa sai a ce yanzu ya zama ma'asumi ba, da ma can su Ma'asumai Allah ya yi su haka nan ne. Shi kuwa abin da muke cewa, su zababbu ne kuma ayyukan daidai da matsayinsu ne.

TAMBAYA: Akwai wani hadisi da aka ce Allah ba ya karbar sallar wandanda suka yi hukunci da abin da ba Allah ya saukar ba. Menene ingancin wannan hadisin, kuma yaya matsayin sallar mutanen Nijeriya da suke bin dimokradiyya?

Daga Ahmad Mando.

SHAIKH ZAKZAKY: Ko ba komai, wannan dai misdakin fadin Allah (T) ne, "waman lam yahkum bi ma anzalallahu…" Saboda haka ka ga ko da ma bai san ingancinsa ba ya san cewa aya ma ta zo da siga shigen irin wannan. Kuma in dai ya fahimci abin da yake nufi, abin da hadisin yake nufi, to sai ya yi kokari daidai gwargwado ya ga ya misaltu da wannan. Amma dangane da hukunta matsayin wani, to wannan ai ba aikinmu bane. Mu ce ai tunda haka aka ce, to wane kaza ne. Shi dai wannan abin da hadisi ya ce kenan kuma ya yi daidai da ma'anar aya.

TAMBAYA: Ya halasta in yi wa yayan mijina sannu da zuwa lokacin da suka dawo daga aiki?

Daga Rufa'atu Aliyu Baba Gusau

SHAIKH ZAKZKY: To ina jin mun sha amsa tambaya shigen irin wannan, kamar wani ya ce ko ya halasta ta yi sallama a amsa masa, ko kaza ko kaza? Akwai magana wadanda ya halasta, wanda ko da a kasuwa ne ko na sayayya da sauransu. Ba inda aka ce in ita matar wani ne ba za ta magana da kowa ba, ban san inda aka sami wannan ba. Sai dai magana wala'alla wanda ya fice kan hanya ne. Amma dai magana ba in da aka ce akwai wani wanda aka ce kar a yi masa magana. Ba wani abu mai kama da haka nan, ballantana har a ce, to wane ana iya ce masa barka da zuwa?

TAMBAYA: Ina zaune ne a Kaduna, amma garin haihuwata Kano. Shin idan na je ganin gida zan yi kasaru?

Daga Ahmad Kaduna.

SHAIKH ZAKZAKY: Eh, idan yanzu ya tashi a mazaunin Kano, yanzu Kano ya zama masa kamar wani gari, bai da gida a can, bai da iyali a can, ba kuma ya tunanin zai koma da zama can, to ya zama wani gari. Amma idan yana da gida yana da iyali da iyali ko kuma a'a aiki ne ya kai shi Kaduna, yana tunanin zai koma Kano din, to ya zama mai gari biyu. Saboda haka in ya je Kano zai cika sallah ne.

TAMBAYA: Ina da mata amma tana kaurace mani wajen kwaciya, shin ya halasta ni ma in hana ta abin da take bukata, kamar abin ci da sauransu?

Daga Ahmad Abdullahi Kaduna.

SHAIKH ZAKZAKY: To, abin da dai aka sani shi ne ciyar da matarka a abin da ake ce ma Isma ya zama wajibi. Wato matukar tana gidanka dole ne ka ciyar da ita. Sai idan ta fita gidan ne ta tafi wani gida, kamar ta koma gidansu, to shi ne wannan ya fadi a kan ka. Saboda haka matukar tana cikin isma din sa, to lallai shi zai biya ta wajibin da ya hau kansa, shi kuma ya bidi ta ba shi wajibin da ya hau kanta. In ta ki sai ya kai kara ko ya dauki wadansu matakai na neman sulhu, amma ba zai hana mata hakkinta ba.

TAMBAYA: Mutum ne yana da 'ya ta isa aure amma bai sami wani dan uwa da ya je yana son ta ba. Shin zai iya ba da ita aure ga wanda ba dan uwa ba?

Daga Sulaiman Musa Bodinga Sakkwato.

SHAIKH ZAKZAKY: To, ina fata dai abin da yake nufi dan uwa musulmi ne. Idan kuwa haka nan ne, ka ga dole sai ya nema mata. Ya yiwu mu a nan kasar ba mu irin hanyoyin sadarwa din nan. Tana iya yiwuwa rashin sadarwa ne, don lallai akwai gwagware masu yawa wadanda suke bidar aure, kila ba su san akwai wata yarinya wadda take ita ma tana bukatar auren bane. In aka sami hanyar sadarwa ko da ta tattaunawa da wadnsu, insha Allahu za a samu. Amma dai bai kamata ya aurar da ita ga kowane irin mutum ba sai wanda ya aminta da addininsa.

TAMBAYA: Akwai wani irin aiki da Kananan Hukumomi suke dauka, ba ka da wani aiki amma duk wata ana biyan ka albashi. Shin yaya matsayin wannan albashin?

Daga Sulaiman Musa Bodinga Sakkwato.

SHAIKH ZAKZAKY: Na san in dai ba ainihin wani shiri ne na almundahana da shi mai daukar ka aikin ya yi domin ba ka aikin ka rinka karbar kudi kawai ba, dole zai zamana in dai an dauke ka aiki ne an cika takardu, ko da kuwa ba ka aikin ya zama cewa an hana maka ka yi aiki, domin wani aikin in ya taso. Amma dai ban san takamaimai abin da yake nufi ba. Illa iyaka dai abin da zan ce shi ne, in da gaske ne akwai wani aiki da za a dauke ka amma ya zama babu aikin yanzun, amma wata rana yana iya tasowa, yana iya yiwuwa saboda wannan, saboda haka kai ma'aikaci ne ko da ba ka yi aikin ba. Alal misali, akwai masu kashe gobara sai su yi wata da watanni ba su kashe wata gobara ba, amma ka ga ai an hana su su je su yi wadansu ayyuka kuma ana biyan su albashi. Kuma ana iya ma samun ma'aikaci wanda aka horar da shi ya zauna ya yi jiran ko-ta-kwana. Saboda haka ka ga in ana hana shi ya yi wani aiki yanzu ka ga za a biya shi albashi. Amma idan shi ya fahimci wannan ba irin wannan bane, illa iyaka yaudara ce aka shirya, shi dai kawai an sa sunan sa ne a rinka ba shi kudi, ba wai domin da ma shi ma'aikaci bane, to ya san shi da wanda ya taimaka masa, lallai abin da suka yi ya saba ka'ida. Saboda haka ka ga abin da yake karba ba halas dinsa ne. Amma kasantuwar ba ya aiki, amma ma'aikaci ne bai maishe da shi laifi ba.

.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din


Teya Salat